Tsadar Dala Zai Hana ‘Yan Najeriya Aikin Hajji A Bana – Hukumar Jin Dadin Alhazzai

images 2024 03 16T072517.692

Ranar 3 ga watan Janairu 2024 ne NAHCON ta bayyana cewa Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanya ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar karshe domin kammala shirye-shirye da amincewa kan yadda aikin Hajji zai kasance.

Kuma a wannan rana ce aka kawo karshen biyan kudade a asusun ajiyar banki na kasa da kasa (IBAN).

Aminiya ta ruwaito cewa, a yayin da hukumar NAHCON ke kokarin kammala shirye-shiryen aikin Hajjin, an samu cikas a wurin biyan kudin abinci da masauki da sufuri a lokacin aikin Hajji sakamakon rashin wadatattun kudade a hannun hukumar aikin Hajji ta Najeriya.

Ana ganin faduwar darajar Naira ne babban dalilin da ya sa har yanzu hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta gaza kammala shirye-shiryenta.

A halin da ake ciki dai kasar Saudiyya ta fara bayar da biza ga wadansu kasashen da ke niyyar tafiya aikin bana.

Mun gano cewa rashin tabbas kan ko Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai amince da ya bayar da tallafin dala ga hukumar aikin Hajjin kasar nan ya sa ake fargabar yiwuwar kara wa maniyyata kudin tafiya sauke farali a bana.

A watan Fabrairu ne NAHCON ta kayyade Naira miliyan 4.8 a matsayin kudin aikin Hajjin na shekarar 2024, inda ta ce an amince da hakan ne bayan ta karya farashin wasu hidimomin da za a yi wa maniyyata a yayin aikin Hajjin.

A lokacin da aka bayyana hakan, farashin dala na N1,410 a kasuwar bayan fage, yayin da take N1,368 a hukumance.

Mafi karancin kudin da za a biya a matsayin kudin tafiya zai kasance Naira miliyan 8.46 ko kuma Naira miliyan 8.2, wanda ya kai dala 6,000 da ake kayyade cewa za a kashewa kowane mahajjaci.

Shugaban hukumar, Jalal Ahmad Arabi, ya ce kudin zai kai “kusan Naira miliyan 6” idan ba don rangwamen da masu kwangilar hidimtawa alhazai suka yi wa Najeriya ba.

Ko da yake, Jalal bai bayyana ko nawa ne kowane mahajjaci zai biya dala ba bayan an yi rangwame.

Farashin dala ya yi tashin gwauron zabi wata daya bayan wannan sanarwar, abin da ya jefa hukumar cikin mawuyacin hali.

Hakan ta sa dole hukumar ta nemi taimakon shugaban kasa don kar a sake karawa maniyyata abin da za su biya domin halartar aikin Hajjin bana.

Kafin yanzu dai Gwamnatin Tarayya ta sha tallafa wa maniyyata da dala, wanda hakan ya sa ake samun saukin kudin tafiya.

Amma tun da aka samu matsala kan farashin kudaden kasashen ketare musamman dala, babu tabbas kan ko gwamnatin za ta iya ba da tallafin a bana.

Yayin da ake fatan gwamnati za ta shiga tsakani ta hanyar ba da tallafin wurin ba da dala a farashi mai rahusa ga hukumar aikin hajji kasar nan, an tseguntawa wa Aminiya cewa babu kyakkyawar fahimta tsakanin fadar shugaban kasa da hukumar alhazan Najeriya NAHCON.

Wannan dalilin ne ya sa NAHCON ta kasa fara biyan hukumomin aikin Hajjin da ke ƙasar Saudiyya da kuma kamfanonin da ke hidima da alhazai makonni biyu da Saudiyya ta fara bayar da biza ga maniyyatan waɗansu kasashe.

Majiyar da ta zanta da Aminiya kuma ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce hukumar na cikin rudani kan yadda za a tafiyar da aikin Hajjin na bana.

Ta ce, “Tunda hukumar ta sanar da kudin aikin Hajjin bana muke jiran Shugaban Kasa ya yanke shawara kan batun tallafin dala amma shiru.

“Rashin ba da tallafin zai janyo babbar matsala ga maniyyata, domin tabbas hakan zai shafi farashin da aka sanar har kuma maniyyata a Najeriya suka bibbiya.

“Ina kyautata zaton cewa gwamnati na yin taka-tsan-tsan saboda cin hanci da rashawa da ya biyo bayan amincewar biyan kamfanonin jiragen sama dala biliyan 24 don ayyukan da suka yi a aikin Hajjin 2023.”

Majiyar ta kuma bayyana cewa wasu sassan kasar nan sun bayyana rashin gamsuwa kan tallafin ba da dala ga Hukumar Alhazan Najeriya, kan hakan ne ake tunanin shugaban kasa ya dakatar da biyan kudaden, kuma har yanzu ba a biya kamfanonin jiragen saman da suka yi aikin jigilar Alhazan Najeriya a 2023 ba.

Majiyar ta ce, ya kamata a ce wakilan NAHCON su kasance a kasar Saudiyya a mako na biyu na watan Ramadan, domin ci gaba da shirye-shirye.

Wata majiya a daga cikin hukumomin jin dadin alhazai na jihohin kasar nan ta shaida mana cewa: “Halin da suke ciki a yanzu shi ne, babu wata ƙwaƙƙwarar magana daga fadar shugaban kasa zuwa ga shugaban NAHCON.

“Har yanzu ana ganin kamar fadar shugaban kasa ba ta da niyyar ba da tallafin da gwamnati ta saba yi, ina ganin har yanzu ba su yanke hukunci kan ko za su bayar ko ba za su bayar ba, wannan shi ne ne tushen jinkirin da aka samu.”

Ta kara da cewa, bayyanar takardar da ta tabbatar da cewa gwamnati na ba da tallafi ga hukumar ta janyo shugaban kasa ya janye duk wani tallafi ga hukumar, sannan kowa na tsoron saka baki domin abin yana neman ya dauki wani abu mai kama da kabilancin addini.

Labarai Makamanta

Leave a Reply