Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Tsadar Abinci Bai Da Alaƙa Da Kulle Boda – Fadar Shugaban Kasa

Mai ba shugaban kasa shawara kan harokin yada labarai Malam Garba Shehu ya ce abu uku ne suka jawo halin tsadar kayayyaki da ake fuskanta amma batun rufe iyakokin kasar ba ya daga cikinsu.

A ranar Laraba ne ‘yan Najeriya da dama suka taso Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a gaba, inda suke ta sukarsa sakamakon tsadar rayuwa a ƙasar.

Ƙarin da aka yi na farashin wutar lantarki da man fetur na daga cikin abubuwan da suka harzuka wasu ‘yan ƙasar suke sukar shugaban inda har wasu ‘yan arewacin ƙasar ke ƙalubalantar shugaban kan cewa ya nuna musu aikin da ya yi musu a tsawon mulkinsa.

Sai dai a ranar Alhamis, shugaban ya bayyana damuwa kan tsadar kayayyakin abinci da ƴan kasar ke kokawa da gwamnatinsa.

Har ma Shugaba Buharin ya ce gwamnatinsa ta damu kan tsadar kayayyakin a daidai lokacin da kullen korona ya ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin wani hali, a wata sanarwa da Malam Garba ya fitar.

Malam Garba Shehu ya zayyana wa BBC dalilai uku da suka sa ‘yan Najeriya suka samu kansu a hali na tsadar rayuwa kamar haka;

  1. Batun taki: Karayar tattalin arziki da annobar cutar korona ta jawo wa kasashe na nesa da kusa ya shafi shigo da ma’adinai da ake amfani da su wajen sarrafa taki.

Hakan ya sa taki ya yi tsada a noman rani har zuwa yanzu, ta yadda wadansu sun noma shinkafa sun rasa takin saka mata dole ta sa suka saida wa makiyaya shinkafar. An yi haka a kasar nan.

  1. Mugunta tsakanin mutane: Akwai ‘yan kasashen waje da ake gani suna yi. Sayen abinci ake yi ana boye shi a kasar nan.

Kuma gwamnati na nan na daukar mataki kan wannan.

  1. Kafa masana’antun shinkafa: An samu ci gaba wajen kafa masana’antun sarrafa shinkafa da yawa a kasar nan. Kamar a Kano akwai wajen 18 wanda kowanne a ciki yana sarrafa shinkafa daga tan 180 zuwa 400 a kowace rana. Suna daukar ma’aikaci bai gaza 200 ba.

Amma yanzu kowa so yake ya ga cewa masana’antarsa ba ta tsaya ba. Kasuwa ake shiga suna zuba kudi ko nawa ne ba ruwansu don su ci gaba da sarrafa masana’antunsu biya suke a ba su shinkafa danya.

Exit mobile version