Tinubu Zai Jagoranci Taron Yaki Da Ta’addanci Na Afirka A Abuja

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kasa Bola Tinubu zai bu?e taron ya?i da ta’addanci na Afirka da za a gudanar a Abuja fadar gwamnatin ?asar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce taron – wanda Najeriya da ha?in gwiwar ofishin ya?i da ta’addanci na Majalisar Dinkin Duniya suka shirya – za a fara shi ranar Litinin 22 ga watan Afrilu.

Manufar taron ita ce ?arfafa ha?in gwiwa don ya?i da ta’addanci a ?asashen Afirka tare da sake fasalin yadda duniya ke kallon ta’addanci a Afirka, da kuma lalubo sabbin hanyoyin magance matsalar a fa?in nahiyar.

Ana sa ran shugabannin gwamnatoci da manyan jami’an gwamnatocin ?asashen Afirka, da wakilan ?ungiyoyin duniya da cibiyoyi, da jami’an diplomasiyya da ?ungiyoyin fararen hula za su halarci taron.

Sanarwar ta ?ara da cewa ana sa ran mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed za ta halarci taron.

”Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu, da sakataren sashen ya?i da ta’adancin na Majalisar Dinkin Duniya, Vladimir Voronkov, za su gabatar da jawabai a wurin taron”, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

Related posts

Leave a Comment