Tinubu Ya Yi Gabas Mulkin Najeriya Ya Yi Yamma – Sanata Ningi

IMG 20240309 WA0082

Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewacin kasa, Kuma Sanata daga Jihar Bauchi, Sanata Abdul Ahmed Ningi wanda ɗan jam’iyyar hammaya ta PDP ne, ya ce abubuwan da shugaba Tinubu ya samu a ƙasa sun tabarbare saboda irin wahalhalun da jama’a ke ciki.

A hirar sa da Buhari Muh’d Fage,Ya ce: ”Bola Tinubu bai fahimci wannan kasar sosai ba, kuma bai fahimci wahalar mulki na kasa irin Najeriyar nan ba. Ba na ganin laifin sa da yawa saboda lokacin da yake neman shugabanci, ba wani alkawari da ya yi tsakanin sa da mutane, kawai mutane sun rufe ido ne sun zabe shi watakil saboda ya goyi bayan Buhari a lokacin da ya ke neman shugabanci, wasu kuma suna ganin ai musulmi ne saboda haka a goyi bayansa ko zai iya ko ba zai iya ba.”

Sanata Ningi ya kuma yi zargin cewa babu wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin mutanen da suka shige gaba wajen neman a zabi Tinubu a Arewacin Najeriya, da kuma shugaban kasa, ta fannin tsare tsaren ayyukan da ya kamata a yi wa yankin a lokacin mulkin sa.

Dan majalisar ya koka da halin da yan adawa suka shiga a majalisar dokokin kasar, wanda ya ce yana faruwa ne saboda yadda aka yi wa yan adawar karfen kafa wajen nadin shugabanni.

Labarai Makamanta

Leave a Reply