Tinubu Ya Bada Umarnin Bude Iyakokin Najeriya

images 2024 03 14T070645.613

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin sake buɗe kan iyakokin ƙasar – ta sama da ta ƙasa – da jamhuriyar Nijar.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce shugaban ya buƙaci a buɗe iyakokin nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne sakamakon taron ƙoli na kungiyar ECOWAS da aka gudanar a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, a Abuja, inda shugabannin suka amince da ɗage takunkuman tattalin arziki da aka kakaba wa wasu ƙasashen ƙungiyar, ciki har da jamhuriyar Nijar.

Ana sa ran ɗage takunkumin zai rage zaman ɗar-dar da bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki tsakanin Najeriya da ƙasashen da ke makwabtaka da ita.

Umurnin da shugaba Tinubu ya bayar ya kunshi matakai daban-daban da nufin maido da alakar da ke tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Daga cikin takunkuman da aka ɗage sun hada da “Buɗe iyakokin ƙasa da na sama tsakanin ƙasashen biyu, da kuma na hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da ke shiga da kuma fita daga Nijar.”

Haka kuma Najeriya ta sanar da ɗage takunkumin hana bai wa Jamhuriyar Nijar wutar lantarki da a baya ta yi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply