?an takarar shugabancin ?asa a inuwar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa shugabannin ?ungiyar Kiristoci ta kasa CAN cewa ba zai sanya batun addini a mulkinsa ba, muddin ya yi nasara a za?en 2023.
Tinubu ya ce shi Musulmi ne sai dai matarsa da ‘ya’yansa duk Kiristoci ne.
Tsohon gwamnan na Legas ya yi wa?annan kalamai ne a Abuja a kokarin nuna wa ?ungiyar CAN cewa yana tare da su kuma bambanci addini ba zai yi tasiri a shugabancinsa ba.
Batun za?in da Tinubu ya yi na Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ya ja hankali da haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan kasar musamman Kiristoci da ke ganin an yi masu rashin adalci.
Sai dai Tinubu ya ce shi burinsa shi ne kafa gwamnati mai nagarta ba wai bisa addini ko kabilanci ko wani abin da mutum ya yarda da shi ba.
Dan takarar ya ce shi mutum ne da ke neman kawo sauyi a Najeriya, shi yasa yake neman ha?in-kan kowa ba tare da nuna banbanci na addini ba, wajen kai kasar ga nasara.
Tinubu ya tausasa zuciyar shugabanni CAN tare da masu al?awarin cewa za su more a mulkinsa.
A wani labarin na daban ?an takarar shugabancin kasar na APC Bola Tinubu ya yi watsi da zargin cewar ba ya martaba addinin kirista.
Za?en da Bola Tinubu ya yi wa tsohon gwamnan jihar Borno Shettima ya janyo muhawara mai zafi a Najeriyar, kasancewar dukkaninsu mabiyan addinin musulunci ne.
Wasu na ganin hakan tamkar rashin adalci ne ga sauran mabiya addinai a ?asar mai mutane masu addinai da yare daban-daban.
A wata ganawa da ya yi da shugabannin ?ungiyar ta CAN ranar Laraba, ya ce za?en da ya yi wa Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ba ya da ala?a da addini.
Ya ce “na za?i Shettima ne saboda ina tunanin wanda zai taimaka min wajen tafiyar da mulki.”
Ya ?ara da cewa “ban ce babu mutumin kirki mabiyin addinin kirista da zan iya ?auka a matsayin mataimaki ba, amma abin da muke bu?ata a yanzu shi ne samun mafita ga matsalolinmu.”