Tijjani Da Bruce Sun Zama Shugabannin Kungiyar Kafafen Yada Labarai

Kungiyar kafafen yada labarai masu zaman kansu na kasa, (IBAN) ta zabi Mr Guy Murray Bruce mamallakin Silverbird TV a matsayin shugaban kungiyar. Inda aka zabi Dr Ahmed Tijjani Ramalan mai kafafen yada labari na liberty TV da radio a matsayin mataimakin shugaba.

Kungiyar IBAN itace jagorar kafafen yada labarai na najeriya masu zaman kansu wadda aka kafa ta a shekarar 1993 lokacin da tsohon shugaban kasar Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida ya bada damar bude kungiyar wadda Chief Raymond Dokpesi mai kafar talbijin na AIT ya fara shugabantar kungiyar a wanchan lokacin.

Nadin nasu ya biyo bayan wani zama na musamman ne da kungiyar tayi a jiya laraba, kuma tsohon shugaban kungiyar Mr Osa Sunny Adun ya mika sakon godiyar sa ga manbobin kungiyar bisa hadin kan da suka bashi yayin jagorancin kungiyar.

Sauran zaben da akayi sun hada da Charles Maraizu a matsayin sakataren kungiyar, sai Hon Habeeb Fasinro a matsayin mai bada shawara kan harkokin shari’a, sai Mr Ime Ufot a matsayin sakataren yada labarai. Sauran nade- naden sun hada da Mrs Tatiana Mousalli Nouri a matsayin Ma’ajin kungiyar, sai Mr Chris Ubosi a matsayin sakataren kudi, da kuma Mr Greg Odutayo a matsayin sakataren gudanarwa.

Daga karshe Sabon shugaban kungiyar Mr Murray da Dr Ahmed Tijjani Ramalan sunyi alwashin bada cikakkiyar gudunmuwar su wurin kawo wa kungiyar cigaba mai ma’ana.

Related posts

Leave a Comment