Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Tasirin EndSARS Ga ‘Yan Najeriya – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce zanga-zangar kyamar rundunar SARS ta sa gwamnati za ta yi gyara ga tsarin ƴan sanda a ƙasar baki daya.

Zanga-zangar da ake kira EndSARS ta ci gaba da bazuwa a sassan Najeriya, inda yanzu ta shiga mako na uku ana gudanar da ita a fadin ƙasar.

  1. A kwanaki goma sha biyu da suka gabata, kasarmu ta fuskanci zanga-zangar matasa daga birane da dama, waɗanda suka nuna rashin jin daɗinsu kan take haƙƙin ɗan Adam da suka hada da azabtarwa, kwace, muzgunawa da tsoratarwa har ma da kisa da jami’an rundunar yaki da fashi da makami ta SARS suka aikata.
  2. Buƙatun neman sake fasalin aikin ƴan sanda da matasa masu zanga-zangar ke yi yana cikin burin ƴan Najeriya da ke cikin taken ƙasa.
  3. Irin wannan hukunci da rashin bin doka ba su dace da tsarin mulkin dimokuradiyyar Najeriya Ba.
  4. Rashin hukunta SARS ya kasance ƙalubalen da matasa suka yi fafutika da ƙwarin guiwa kuma suka yi nasara wanda ya haifar da tunanin sake fasalin tsarin ‘yan sanda a kasar.
  5. Dole ne masu zanga-zangar su amince cewa matakin da gwamnatin Shugaba Buhari ta ɗauka ya cancanci yabo, ba wai kawai rusa SARS ba har da yarda da bukatu biyar da suka haifar da zanga-zangar.
  6. Duk da yake a baya gwamnati ba ta aiwatar da sauye-sauyen da ta yi alkawari ba, amma yadda wannan gwamnatin ta yi hanzarin sauraren buƙatun masu zanga-zangar a wannan karon yana nuna cewa akwai kyakkyawan sauyi daga gare ta da kuma wani sabon yanayi na magance matsalolin Al’umma.
  7. Dole ne a bai wa gwamnati dama don ta aiwatar da sauye-sauyen da masu zanga-zangar suka nema. Tabbas ba za a iya aiwatar da su ba nan take sai anyi nazari akai kafin a aiwatar.
  8. Masu zanga-zangar sun samu nasarori masu yawa cikin kankanen lokaci. Amma kuma ya kamata su yi hankali kada su ɓata rawarsu da tsalle musamman yadda wasu zauna gari banza da ƴan daba ke neman kwace zanga-zangar don tayar da hankali da cin zarafin mutane a kasa.
  9. Dole ne sai masu zanga-zangar sun yi hankali kada su samar da wani yanayi na tarwatsa tsarin dimokuradiyya da ya ba su dama da ‘yancin yin zanga-zanga.
  10. Ina kira ga shugabannin addini da su yi kira ga mabiyansu su janye zanga-zangar a yanzu a samu zaman lafiya a kasa.
Exit mobile version