Tashin Dala: EFCC Ta Damke ‘Yan Canji A Biranen Abuja Da Legas

Hukumar Yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta kama ‘yan canji 87 a babban birnin kasar Abuja da kuma jihohin Lagos da Kano a ci gaba da kokarin kawo karshen matsalar karanci da tashin farashin Dala da ake fuskanta a kasar.

An ruwaito cewar jami’an hukumar EFCC sunyi dirar mikiya a wasu daga cikin wuraren canjin kudi da ke Abuja tare da kama mutane 25 masu gudanar da harkar ta haramtatciyar hanya wanda ya ke zuwa bayan kama wasu 40, adadin da ya nuna cewa mutane 65 ke nan hukumar ta kama a Abuja.

Haka nan jami’an hukumar sun kama wasu ‘yan canji 14 a jahar Lagos da kuma wasu mutane 8 a kasuwar canjin kudi ta Wapa da ke jahar Kano.

Duk da yake babu wasu dalilan game da kamen da hukumar ta EFCC ta bayar, amma ana ganin hakan nada alaka da kokarin bin diddigin asalin kudaden da ake tunanin ‘yan ta’adda da wasu ‘yan siyasar kasar za su fiddo don sauya su zuwa kudaden ketare ganin umarnin babban bankin kasar CBN na sauya fasalin wasu takardun kudin kasar a watan gobe.

Dama ko a ranar Talatar nan sai da shugaban hukumar ta EFCC AbdulRasheed Bawa ya gana da kungiyar shugabannin bangaren bin ka’ida na bankunan kasar da shugabannin kungiyar ‘yan canji ta kasar da sauran masu ruwa da tsaki game da lamarin a jihar Lagos.

Labarai Makamanta

Leave a Reply