Tashin Bam Ya Hallaka Jama’a A Jihar Borno

IMG 20240229 WA0096

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Maiduguri na jihar Borno na bayyana cewa Bam din ya fashe ne lokacin da wani labura ya dauko bulolluka zuwa wani bangare na wata makaranta ashe bai san ya na dauke da bam din ba.

Majiyar ta ce bam na biyu kuwa ya fashe inda ya hallaka wani lebura a bayan garin Koibe da ke jihar. ZagazolaMakama ta tabbatar da cewa bayan mutuwar mutanen biyu, akalla mutane shida ne suka samu munanan raunuka.

A watan Janarun wannan shekara, bam ya tarwatse da wasu yaran Islamiyya a karamar hukumar Gubio da ke jihar. Matakin da Zulum ya dauka kan ‘yan bola jari Akalla yara guda shida ne suka mutu yayin tarwatsewar bam din wanda aka yi tsammanin kayan karfunan bola jari ne.

A shekarar 2023 ce Gwamna Babagana Zulum ya dakatar da dukkan ayyukan ‘yan bola jari a dukkan kananan hukumomin jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply