Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Tarwatsewar Najeriya: Dattawan Arewa Sun Kalubalanci Osinbajo

Kungiyar dattawan arewa, ta soki mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kan jawabin da ya yi na cewa rabuwar kan da aka samu a Najeriya a yanzu zai iya sanadin tarwatsewar kasar.

A yayin da kungiyar ta amince akwai rabuwar kai a Najeriya, ta ce bai dace mataimakin shugaban kasar ya rika fadin kalaman da za su kara janyo tabarbarewar lamarin ba.

Dattawan sun gargadi Osinbajo akan furta kalaman da za su kara tada hankali a kasar.

Osinbajo wanda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya wakilta a wani taron coci da aka yi a ranar Lahadi a Abuja don murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yanci ya ce, “Katangan mu bai rushe ba tukunna, amma akwai wuraren da suka tsage kuma idan ba gyarawa aka yi ba za ta rushe.”

Kungiyar Dattawan arewa ta amince akwai baraka a kasar amma ta ce kasar za ta farfado ta dinke barakar.

A hirar da ya yi da Sakataren watsa labarai na Ƙungiyar Dattawan Arewa Emmanuel Yawe ya gargadi sauran shugabanin kasar su ‘kula da irin abinda suke fadi’.
“Akwai baraka amma muna tsamanin mataimakin shugaban kasar ya kwantar da hankulan mutane ne ba ya fadi abinda zai harzuka su ba.
“Muna fatan cewa Najeriya za ta magance matsalolin da suke addabar ta kamar yadda ta yi a baya don kare abinda zai janyo ta ruguje.

Domin cimma hakan, Shugabannin a Najeriya irinsu Osinbajo su kula da abinda ke fitowa daga bakinsu.”

Exit mobile version