Tarar Miliyan Biyar: Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai Ta Buƙaci NBC Da Cika Sharudda

Ƙungiyar kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu ta ƙasa, ta buƙaci hukumar kula da Kafafen yaɗa labarai ta ƙasa NBC da yin duba akan wasu dokoki na hukumar kafin ƙakaba tarar Naira miliyan biyar da ya sanya wa ɗaya daga cikin ‘ya’yan kungiyar, gidan rediyon Nigerian Info FM, bisa ga zargin gidan rediyon ya yaɗa labaran da basu kamata wanda ka iya da rikici.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a yayin wani taron gaggawa da ta kira ranar Litinin domin duba wannan lamari a ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar Mista Guy Murray- Bruce.

“Da akwai wasu sharudda guda uku da muke bukatar hukumar NBC ta cika su kafin sanya wannan tara ta Miliyan Biyar da ta yi.

1- Naira miliyan biyar da hukumar ta sanya a matsayin tara ga yaɗa kalaman ɓatanci na cikin dokokin hukumar ne wanda ba’a kaddamar da aiki da shi ba, bisa ga haka ya zama wajibi ga hukumar ta duba wannan ɓangare ta tabbatar da dokar tukuna, kafin zartar da ita.

2- Lallai ne a fili yake dangane da batun da ake ciki, Hukumar NBC ta zama mai ƙara da zama Alkali a lokaci guda ba tare da bada dama na sauraren sauran ɓangare ba.
Dole ne hukumar ta fayyace menene kalaman ɓatanci, kuma ya zamana tarar kuɗin dukkanin ɓangarorin yaɗa labarai sun haɗu akai.

3- Kamar yadda muka sani shine aikin Jarida na tafiya ne akan gudanar da bincike da bankaɗo abubuwa da kuma bada kariya ga ‘yan jaridar gaba ɗaya.

Bisa ga haka muna kira ga Hukumar BBC da ta samu zama da mahukunta s ɓangaren yaɗa labarai waɗanda suka haɗa da ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa NUJ da kungiyar Editoci, da kamfanin dillancin labarai na kasa da sauran su domin duba yadda tsarin dokar tara take ga abin da aka amince cewa kalaman ɓatanci ne.

Labarai Makamanta

Leave a Reply