An ruwaito cewa mutum biyar sun rasa rayukansu nan take yayin da suke ?o?arin jidar kayayyakin tallafin CORONA da rabon wani adadin kudi da suka tsinta a ma’ajiyar abinci na gwamnati a Jalingo, jihar Taraba.
An ruwaito cewa mutanen sun ?alle wurin ajiyar abincin ne inda suka tsinci jakuna biyu ?auke da ku?i ?ab dubu-dubu kusa da sakatariyar Kungiyar Kiristoci ta Najeriya a Jalingo ranar Asabar.
Daga nan ne suka yi watsi da abincin suka fara kokowar yadda za su raba ku?in da suka tsinta. Mutum 5 sun mutu yayin rabon ku?in da suka tsinnta a ma’ajiyar kayan tallafin korona.
An ruwaito cewa mutanen da abin ya faru da su sun mutu yayin da dubban mutane suka yi ?o?arin kokawar ganin suma an raba ku?in tare da su.
An gano cewa duk da mutum 5 sun mutu yayin ?o?arin rabon ku?in wasu jami’an tsaro suma sun shiga kokawar. An gano cewar an ajiye kayan abincin a da?in ajiyar tun watanni hudu da suka gabata.
Rahotanni sun ce mutane maza da mata sunyi ta ?ibar kayan abincin wasu ma da ababen hawa suka taho.
Wasu cikin masu ?iban kayan da aka tattauna da su sun ce da ku?in al’umma ne aka siya kayan abincin. Wata mata ta ce, “muna kwasar kayan mu, ?an siyasar nan azzalumai ne don sun ?oye abincin duk da sun san mutane na fama da yunwa.”
Da aka tuntube shi, sakataren dindindin na hukumar bada agajin gaggawa na jihar Taraba, Danazumi Navulga ya ce ba zai yi tsokaci kan lamarin ba don ya yi murabus.