BASHIR ADAMU, JALINGO
Rahotannin dake zuwa mana yanzu daga Jalingo babban birnin jihar Taraba na cewa ana zargin wasu mafusatan Matasan APC sun lakadawa Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Taraba, Barista Ibrahim Tukur El-Sudi dukan kawo wuka, jim kadan bayan kammala ganawar sirri na masu ruwa da tsaki a zaben fidda gwani na Gwamna a Jam’iyyar.
Rahoton ya kara da cewa hakan ya biyo bayan wasu makudan kudade ne da Matasan suka gani makare a cikin Motar Shugaban Jam’iyyar da suke zargin cewa kudaden cin hanci ne ya karba a hannun wani Dan-takara da nufin goya masa baya.
Inda majiyar ke cewa, da kyar Jami’an ‘Yan Sanda suka kubutar dashi a hannun mafusatan matasan Jam’iyyar ta APC.
Wakilinmu ya tuntubi Sakataren Jam’iyyar APC Jihar Taraba, Mista Aeron Artimas dangane da faruwan lamarin, sai yace ‘lallai hayaniya ta kaure a wurin, kuma hayaniya a fagen Siyasa ba wani abu bane saboda an sha samun hargitsi makamancin haka a ko ina, a fagen siyasa har takan kai ga sai an garzaya Sakatariyar Uwar Jam’iyya domin shiga tsakani.
‘Amma babu wanda ya doki Shugaban Jam’iyyar tasu Ibrahim Tukur El-sudi’, kuma maganan zargin ganinshi da makudan kudi, ai yanzu Duniya ta cigaba, ba sai anyi yawo da kudi a fili ba, akan iya turawa ta yanar gizo, wato transfer’.
Na kuma tambayi Aeron Artimas, ko wani hali suke ciki dangane da fara gudanar da zaben a yanzu, sai yace ‘bazan iya cewa komai ba, don ba APC Jaha ce take shirya zaben ba, Uwar Jam’iyyar su ta Kasa ce ta turo Kwamitin zaben, saboda haka in nemosu duk inda suke su bani bayani’.
Hardai izuwa lokacin wannan rahoton, babu dan Kwamitin gudanar da zaben Gwamna na APC Jihar Taraba, ko guda daya da ya bayyana kansa.
Daga bisani, na tuntubi Kakakin Yansandan Jihar Taraba, DSP Abdullahi Usman domin jin tabbacin aukuwan lamarin, sai yace ‘a halin yanzu dai ina zaune a Ofishina dake Sharkwatan Yansandan Jihar Taraba, kuma har yanzu labarin bai riga yazo mini ba.