Taraba: Kotu Ta Kori Timothy Hamman Daga Jagorancin Kungiyar Taraba FA

BASHIR ADAMU, JALINGO

Babban Kotun Gwamnatin Tarayya dake da zamanta a Jalingo ta kori Timothy Heman Magaji, inda ta tabbatar da Sanusi Mahmud a matsayin sahihi kuma zababben Shugaban Kungiyar Kwallon Kafan Jihar Taraba, wato Taraba FA a turance.

Wakilinmu Bashir Adamu daya halarci zaman Kotun ruwaito mana cewa;

Bayan daukan tsawon lokaci yana karantawa tare da nazari akan hukuncin, Mai- Shari’a, Simon Akpah Amobeda daya jagoranci Shari’an ya Umurci Timothy Magaji da nan take ya fice daga wannan Ofishin kuma kar ya sake aiyana kanshi a matsayin Shugaban Kungiyar ta Taraba FA.

Mai- Shari’a Amobeda, ya kuma umurci Kungiyar Kwallon Kafan Najeriya (NFF) da nan take ta amince da Sanusi Mahmud a matsayin Shugaban na Taraba FA.

Idan-dai za’a tuna, tun a ran 12 ga Watan Junin, Shekara na 2019 ne Kungiyar ta tsunduma cikin rikicin Shugabanci, a lokacin zabubbukan Shuwagabannin ta.

Tun wannan lokacin ne, Sanusi Mahmud ya kalubalanci sakamakon zaben da ta tabbatar da Timothy Heman a matsayin wanda yayi nasaran kasancewa Shugaban Kungiyar a Kotu tun a shekara ta 2020.

Barista Isa Buba, shine Lauyan wanda ya shigar da kara, Sanusi Mahmud da yayi nasara a Shari’an, inda yake cewa “nayi matukar farin ciki da wannan nasara da mukayi a Shari’an, hakan ya samu ne bisa kwararan hujjojin da muka gabatarwa Kotu.

A cewan Alkalin, Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa, NFF tayi sakaci na rashin bincike na hakika kan yanda zaben ya guda, wanda da’ace tayi haka, da baika ga zuwa wannan Kotunba.

Da wannan ne Mai Shari’a, Amobeda ya yanke wannan hukuncin tabbatar wa Sanusi Mahmud Kugeran Shugabanci Kungiyar Kwallon Kafan Taraba, wato Taraba FA, tare da cin taran wadanda aka kai kara Naira Miliyon Biyu, kudin bata lokaci da wahal-halun da Sanusi Mahmud yayi na kara”.

Duk kokarin da nayi domin jin ta bakin wadanda ake kara ya ci tura, sakamakon kin amincewa suyi magana dani.

Related posts

Leave a Comment