TARABA: Hukumar Jin Dadin Alhazzai Ta Sanar Da Kudin Ajiyan Maniyyata

BASHIR ADAMU, JALINGO

Rahotannin dake shigomana yanzu daga Jihar Taraba na cewa, Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar ta sanar da Naira Miliyan Biyu da Dubu Dari Shida, a matsayin kudin ajiya da Maniyyata aikin Hajji na bana zasu biya a Jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takardan sanarwa dake dauke da sa hannun Sakataren Gudanarwar Hukumar, Alhaji Umar Ahmed Ciroma da aka rabawa manema Labarai a Jalingo fadan Jiha.

Sanarwan ya kuma umurci dukkanin Maniyyata aikin Hajjin na bana, musamman wadanda basu sami daman tafiya ba a shekaran daya gabata na 2022 da su gaggauta biya kafin 30 ga wannan Watan da muke ciki.

Har ila yau sanarwan yaja kunnen Maniyyata da su guji biyan Kudi a asusun bankin dai-daikun mutane ba’a na Hukumar ba, tana mai cewa duk wanda ya ko ta aikata hakan, su sani sunyine don kashin kansu bada yawun Hukumar ba.

A baya dai, a kalla Maniyyata aikin Hajjin 1,700 daya kamata su tafi a Shekaran 2022, amma sakamakon karancin gurbin Kujeru da Hukumar Aikin Hajjii ta Kasa (NAHCON) ta warema Jihar da kuma karin Kudin tafiyar ya sanya dayawa basu iya tafiya Aikin Hajjin ba a bara.

Labarai Makamanta

Leave a Reply