Kungiyar MURIC mai kare hakkin musulmai a Najeriya, ta zargi gwamna Darius Dickson Ishaku na jihar Taraba da daukar musulmai a matsayin saniyar ware.
MURIC ta ce gwamnatin mai girma Darius Dickson Ishaku ta dauki duk Kiristoci da Jukunawa a matsayin ‘yan lele wajen raba duk wata dama da aka samu a Taraba.
Daraktan MURIC na kasa, Farfesa Ishaq Akintola ya bayyana wannan a safiyar ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, 2020, a wani jawabi da ya aikawa jaridar Daily Nigerian.
Akintola ya ke cewa: “Mu da dalilin da zai sa mu binciki ayyukan gwamnan Taraba Ya na danne musulman jihar da wadanda ba Jukkunawa ba.
Farfesan ya ce: “A karkashinsa (Darius Ishaku), an kiristantar da duk wasu bangarorin gwamnati. Daga harkar ilmi zuwa daukar aikin yi da rabon mukaman siyasa.
Ba a sa Musulmai da wadanda ba su fito daga cikin kabilar Jukun ba a cikin lissafi.” Inji MURIC.
Kungiyar ta ce shekaru biyar kenan ana fama da kullaliyar manakisa da kiyayya da ake nunawa Musulmai da fifita Kiristoci da Jukkunawa a Taraba a kan duk sauran kabilu.
Musulman Taraba su na fuskantar wariya idan aka zo maganar shiga makarantun gaba da sakandare. Ana ware damar karatu kyauta ne ga Kiristoci kurum.
Jawabin da ya kara da cewa: “Ana yawo da takardun bada aiki a boye a coci, fastoci su na ba mabiyansu takardar sa hannu wanda ake ba su aiki da zarar sun gabatar da ita.
Karin matsaya a wurin aiki ya danganta ne da addinin mutum. Har kudin Musulman ma’aikatan da su ka mutu ba su fitowa daga hannun gwamnati, amma ana biyan iyalan kiristoci.
Dole MURIC ta binciki gwamna Darius Ishaku. Musulman Najeriya su na so su san meyasa Kwamishinoni 10 daga cikin 14 a jihar kiristoci ne a yayin da musulmai su ke da rinjaye a kananan hukumomi 12 a cikin 16 da ake da su.
Meyasa shugabannin jami’o’in jiha, da makaruntun koyon aiki da kwalejin ilmi da makarantun koyon aikin jinya da na fasaha duk su ke hannun Kiristoci.
Kungiyar ta bukaci gwamnan ya yi wa jama’a bayani tun da sauran Musulman jihar Taraba su na hakkin a dama da su. MURIC ta bada shawarar a gyara wannan domin samun zaman lafiya.