Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana shirin bayar da tallafin kudi na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin yaudara. Gwamnatin Tinubu ta ba da shawarar rabawa iyalai miliyan 12 N8,000 na tsawon watanni shida don rage masu radadin cire tallafin man fetur da aka yi.
Da yake magana a wata hira da Arise TV a daren ranar Juma’a, 21 ga watan Yuli, Sani ya bayyana cewa babu wani sahihin bayanai na wadanda za su amfana daga shirin. “Matsayina a kodayaushe ya kasance cewa, a wannan mawuyacin lokaci, kada batun raba kudi ya zama abun da za mu kawo cikin lissafi. Ina ganin shirin rabon kudi a ganina, a ra’ayina, damfara ce. Yaudara ce gaba daya. Zan iya tabbatar da hakan sosai.
Sai dai kuma, gwamnan ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta fara tabbatar da ganin cewa an kula da mutanen da aka tsame daga cikin shirin kudin musamman a arewa maso yamma sannan a kawo tsarin kudi kafin aiwatar da shirin bayar da tallafin kudin.
“Mu kara zuba karin kudi don mu tabbatar mun bude musu asusu, mu sanya su a ciki, idan ba mu yi haka ba, duk abin da muka yi duk yadda ka yi, kudin zai shiga hannun mutanen da ba su dace ba, gaskiyar magana ke nan,” inji shi.