Taliban Ta Bada Umarnin Rufe Kantunan Kwalliya Da Gyaran Gashi A Afghanistan

?an Taliban sun ba da umarnin rufe wuraren kwalliya da na gyaran gashi a ?asar Afghanistan a wani sabon tarna?i da mata ke fuskanta.

Wani mai magana da yawun ma’aikatar kula da harkokin kyautata ?abi’u ya shaida wa BBC cewa kantunan suna da wata ?aya su yi biyayya da umarnin, daga ranar 2 ga Yuli da aka fitar da sanarwa.

?an Taliban dai tuni suka haramta wa ‘yan mata da mata daukar karatu a azuzuwa da zuwa wuraren motsa jiki da na sha?atawa, kuma a baya-bayan nan ma sun hana mata yin aiki da hukumomin Majalisar ?inkin Duniya.

Hukumomin na Afghanistan sun kuma ba da umurnin cewa mata su dinga sanya suturar da za ta bayyana idanunsu kadai, kuma dole ne su kasance tare da muharraminsu a duk lokacin da suka yi tafiya ta sama da kilomita 72.

Rufe wuraren kwaliya da gyaran gashi, wani ?angare ne na matakan da ‘yan Taliban suka ?auka a lokacin da suka yi mulki na ?arshe tsakanin 1996 zuwa 2001. Amma sun sake bude wuraren bayan mamayar da Amurka ta yi wa Afghanistan a shekara ta 2001.

Related posts

Leave a Comment