Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi bayanin cewa matsalar talauci ba ƴan Najeriya kaɗai ta shafa ba Shugaba Tinubu ya bayyana cewa akwai talauci da wahala a ƙasar nan amma hakan matsala ce wacce ta shafi dukkanin duniya ba Najeriya kaɗai ba Ya yi nuno da cewa dole ne a magance matsalar ayyukan ƴan bindiga da ta’addanci domin manoma su samu damar noma abinci a gonakinsu
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ba ƴan Najeriya ne kaɗai ke fuskantar talauci a duniya ba. Shugaban ƙasan wanda ya amince cewa akwai talauci da wahala a ƙasar nan, ya ce dole ne a magance ƙalubalen.
Ya yi bayanin cewa ɗaga cikin hanyoyin magance ƙalubalen ita ce kawar da ƴan bindiga da ƴan ta’adda ta yadda manoma za su iya komawa gona.
Tinubu ya gana da ƴan majalisa
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata, Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƴan majalisar tarayya, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Tawagar ta samu jagorancin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, mataimakinsa, Barau Jibrin da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu da sauransu, rahoton The Punch ya tabbatar.
“Eh akwai talauci, ana shan wuya a ƙasar nan. Ba mu kaɗai ba ne ke fuskantar hakan, amma dole ne mu fuskanci ƙalubalenmu.” “Dole ne mu samo hanyar da za mu kawar da ayyukan ƴan bindiga da ta’addanci ta yadda manoma za su iya noma abinci a gonakinsu.”
Idan babu hanyoyi masu kyau da za a kawo abincin ga jama’a, ko da an noma abincin amma ana yin asarar kaso 60-70%, za a samu babbar matsala.”