Takurar Legas Da Abuja Ne Ya Sa Tinubu Tafiya Landan – Kakakin Tinubu

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar lokacin da aka fara yakin neman zabe, sai ga shi Asiwaju Bola Tinubu mai neman shugabancin Najeriya a inuwar APC mai mulki ya bar kasar lamarin da ya haifar da surutai a ƙasa.

Da aka zanta da Ayo Oyalowo mai magana da yawun Tinubu a gidan talabijin na Arise TV, ‘dan siyasar ya bayyana abin da ya sa ‘dan takarar na su ya tafi Ingila, ya kuma ce lafiyansa lau, kawai ya tafi hutu ne.

Ayo Oyalowo ya bayyana cewa Bola Tinubu ya tafi birnin Landan ne da nufin ya huta domin a nan Najeriya, jama’a ba za su kyale shi ya samu damar hutu ba. Ba za su bar shi ya samu hutu ba “Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana London. Ba zai iya hutawa a Legas ba, ko Abuja ba za su bar shi ya huta ba”.

“Saboda haka sai mutane masu hankali suka ga ya kamata ya samu hutu tun da lokacin kamfe ya karaso.” Saboda haka an gayyaci Bola Tinubu wajen yarjejeniyar zaman lafiya ne bayan ya bar Najeriya, ya tafi ketare birnin Landan domin samun hutu.

“A sa’ilin da goron gayyatar ya zo, shi kan shi Kashim Shettima ya na Maiduguri, amma dolensa ya kama hanya ya dawo Abuja a lokacin. “Goron gayyatar yarjejeniyar zaman lafiya ya zo ne bayan Tinubu ya fice daga kasar nan. Shi kan shi abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima bai gari a lokacin, sai da ya bar abin da yake yi a Maiduguri.”

Oyalowa wanda yana cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben APC ya karyata rade-radin cewa ‘dan takararsu ya na asibiti inda ya bayyana cewar Tinubu garau yake.

Labarai Makamanta

Leave a Reply