Wani rahoto da jaridar Bloomberg da ke Amurka ta fitar ya bayyana takardar kudin Najeriya wato Naira a zaman daya daga cikin wadanda darajarsu ta fi faduwa a duniya yanzu.
A cewar rahoton darajar Nairar ta fadi da kusan kashi 37% a wannan shekarar kawai.
A cewar rahoton, Naira ita ce takadar kudi kasa ta biyu darajarta ta fi faduwa a Nahiyar Afrika inda ka cire takardar kudin Cedi ta Ghana wadda darajarta ta fadi da kashi 55% a bana.
Wadanda ke bi ma Nairar wajen faduwar darajar a Afrika sun hada da Leone ta kasar Saliyo wadda darajarta ta fadi da kashi 36% da kuma Fam din kasar Masar wadda ta rasa kashi 35% na darajarta.
Sai dai wani akasi inji rahoton darajar Naira na da armashi sosai har yanzu a canjin gwamnati domin darajar ta fadi ne da kashi 4% dari kawai kan dalar ta Amurka duk karfinta a bana.
Wanda hakan ke nufi Naira tana gaba da dalar kasar Canada da Franc ta kasar Siwizland wajen rike darajarta a kan kudin na Amurka.
Babban bankin Najeriya dai ya kayyade yawan dalar yake sayar wa kowane rukuni na masu bukatarta a kasar, abin da ya sa kamfanoni da daidaikun jama’a komawa nemanta a kasuwar da ba ta hukuma ba.
Wannan in ji rahoton shi ya sa aka samu bambacin kashi 90% dari tsakanin yadda gwamnati ke canzar dalar a Najeriya da kuma yadda ake canza ta a wuraren canjin kudi masu zaman kansu.
Rahoton ya ambato wani dan canji a babban birnin kasuwanci kasar Legas na cewa an rufe kasuwar canji a hukumance dalar na kan Naira 442 da kobo 75, a daidai lokacin da take canza ta kan naira 890 a gefe titi.
Darajar Naira ta fara rikitowa ne kwana daya bayan da babban bankin ya sanar da cewa zai canza kudin kasar a wani yunkuri na rage yawan takardun kudi a bainar jama’a.
Jaridar ta ambato wani masanin tattalin arziki a kasar na cewa mai yiwuwa darajar kudin kasar ci gaba da faduwa saboda raguwar kudaden shiga da kasar ke samu daga sayar da danyen mai da kuma karuwar fitar da kudi daga kasar saboda rashin tabbas da ke tattare da zaben shugaban kasa da za a yi a watan Febrairu.