Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Damaturu cikin jihar Yobe ta tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halartaccen dan takarar sanata na jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa.
Jam’iyyar APC mai mulki ce ta miƙa sunan shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Lawan ga hukumar zaɓe a matsayin ɗan takarar sanata mai wakiltar Mazaɓar Yobe ta Arewa maimakon Bashir Machina, wanda ya ci zaɓen fitar da gwani na mazaɓar.
Abdullahi Adamu ya yi iƙirarin cewa Sanata Ahmad Lawan ya sayi fom kuma ya shiga zaɓen fitar da gwani na sanatan Yobe ta Arewa, sai dai Bashir Machina ya ce shi kaɗai ya tsaya takara a zaɓen.
Sai dai a ranar 21 ga watan Yunin 2022, Bashir Sheriff Machina ya garzaya gaban kotu, yana kalubalantar matakin jam’iyyar APC na aika sunan Sanata Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar sanata na mazabar Yobe ta Arewa.
Tun farko dai ya ce ba zai sauka ko janyewa kowa takararsa ta majalisar dattijai ba.
Tun bayan rashin nasara da ya yi a zaben fitar da gwani na takarar shugaban ƙasa a APC, aka fara takaddama kan makomar siyasar Sanata Ahmad Lawan bayan ya shafe fiye da shekara 20 yana wakiltar al’ummarsa a Majalisar Wakilai da ta Dajjitai.
Wannan hukunci na babbar kotun tarayya a ranar Laraba na nufin Ahmad Lawan ya rasa dama ta yiwuwar komawa majalisar dokokin Najeriya.