Takaita Cire Kudi Zai Rage Wa ‘Yan Siyasa Sharholiya – Sanusi


Khalifa Muhammad Sanusi , ya ce matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na takaita cirar kudaden zai fi yin tasiri a kan `yan siyasa kasar fiye da talakawa.

Ya bayyana hakan ne a karshen karatun Madaris da ya saba yi duk karshen mako.

Ya ce `yan siyasar kasar na amfani da kudi a lokacin zabe don sayen kuri’un jama’a, lamarin da ke haifar da koma-baya ga kasar.

Muhammadu Sanusi na II ya ce “abin takaici ne yadda mutane za su yi shekara hudu suna kwasar dukiyar al’umma, suna barin mutane a cikin wahala da yunwa, sannan su fito da irin kudaden su sayi kuri’u, su biya ‘yan sanda, da DSS, da ma’aikatan INEC da `yan daba a sayo musu kwaya, a saya musu makamai, don hana mutane zabe.”

Haka kuma tsohon Sarkin na Kano ya ce wannan tsari da CBN ya fito da shi shi ne zai fara rage barnar da ‘yan siyasa ke yi kuma zai takaita magudin zabe.

A cewarsa, matakin na CBN tsari ne da aka jima da fara aiwatar da shi a Najeriya shekaru 10 da suka gabata a lokacin da yake gwamnan babban bankin kasar.

Sannan ya ce a lokacin da yake gwamnan bankin Najeriya shi ya fara aiwatar da tsarin takaita yawan garin kudi a Najeirya a hannun jama’a, inda suka fara da jihar Lagos sannan daga bisani suka fadada shi zuwa jihohi biyar da Abuja.

“Duniya tana canjawa, muna so tsarin kudi a hannun `yan Najeirya ya zama mai sauki, kuma a rage sata, sai dai a lokacin da ka fara mutane suka yi ta hayanayi cewar ba sa so, amma ga shi yanzu an fara fahimtar amfaninsa.”

Dokar takaita cirar kudin da Babban Bankin Najeriya, CBN, ya fitar a ranar 6 ga watan Disambar da muke ciki, za ta fara aiki ne daga ranar 9 ga watan Janairun shekarar 2023.

Sannan kowanne mutum iya  naira dubu 20 kadai zai iya fitarwa daga banki a rana daya, a mako kuma naira dubu 100.

Haka kuma dokar ta ce duk wanda ya je cire kudin da suka haura naira dubu 50 da cekin bankin da wani ya rubuta masa, ba za a ba shi kudin ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply