Babban hafsan rundunar sojojin kasa na Najeriya (COAS), Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce an fi samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yanzu idan aka kwatanta da shekarar 2014.
Buratai ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar jaje wurin wasu sojoji da suka samu raunuka a jihar Kaduna.
Kalaman na Buratai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu mutane ke ganin cewa Najeriya na fuskantar babbar barazanar tsaro sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da mayakan kungiyar Boko Haram, musamman a arewacin Najeriya.
Manema labari sun halarci asibitin rundunar soji da ke Kaduna domin shaida yadda ake duba lafiyar dakarun soji da suka samu raunuka yayin atisaye daban – daban a fadin kasa.
Da yake bayyana jin dadin kasancewa tare da sojojin da suka samu raunuka, Buratai ya bawa sojojin tabbacin cewa kishinsu da kokarinsu na tabbatar da an samu tsaro a kasa ba zai fadi kasa a banza ba.
Na yi matukar farin cikin sake ganinku, na hadu da wasu a cikinku a filin yaki kuma na ga irin kwarfin gwuiwar da kuke da shi. Wannan shine farashin da kuka biya don kishin kasa.
Ina mai alfahari da ku, kokarinku ne yasa ake samun zaman lafiya a kasa, ina mai farin cikin cewa yanzu an samu zaman lafiya a Najeriya idan aka kwatanta da shekaru biyar da suka gabata,” a cewar Buratai.