Ta’addanci Zai Zamo Tarihi Wata Rana A Najeriya – Babangida

Tsohon Shugaban ƙasa na Mulkin Soja Janar Ibrahim Babangida ya bayyana yakinin shi da cewar wata rana matsalolin da suka addabi Najeriya na taɓarɓarewar tsaro da ta’addanci zasu zamo tarihi tamkar ba su taɓa faruwa ba.

Tsohon Shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati, da dagewa wajen yin addu’o’i gami da mayar da al’amurra ga Ubangiji Allah, babu shakka Allah maji rokon bawa ne kuma da yardar Allah komai zai zamanto cikin sauki.

Babangida wanda ya bayyana hakan a yayinda yake jawabi a wata hira da gidan Talabijin na Channels ya yi dashi a sakon shi na sabuwar shekara ta 2021 ya bukaci ‘yan kasa da su zamo masu hakuri da jajircewa domin taimakon Allah na kusa.

A cewar tsohon shugaban kasar, duk abinda yayi farko zai yi karshe. Ya ci gaba da bayyana cewa da zaran ‘yan Najeriya sun zage damtse wajen aiki don cimma manufa, kowa zai ji dadi a 2021.

Yayinda yake karfafa wa ‘yan kasa gwiwar tallafawa gwamnati wajen magance matsalolin da ke da nasaba da jagoranci, Babangida ya bayyana cewa cutar COVID-19 ta shafi duk wani bangare na gwamnatin Najeriya.

Ya yi bayanin cewa annobar ta kawo babban kalubale ga duniya baki daya, ciki harda kasarmu Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply