Ta’addanci: Sama Da Mutane Miliyan Biyu Sun Zama ‘Yan Gudun Hijira

Ministar agaji da kare aukuwar ibtila’i ta Nijeriya Sadiya Umar Farouk, ta ce yanzu haka kasar na da yawan mutane sama da miliyan biyu da suka rabu da muhallansu.

Ta ce wadanda abun ya shafa sun rasa muhallan nasu ne ta sanadiyyar ayyukan ta’addanci da ‘yan bindiga ko kuma rikicin kabilanci.

Ministar ta fadi haka ne a lokacin da take ganawa da ‘yan jaridar fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, bayan wata ganawa da ta yi da shugaba Buhari a Abuja.

Sadiya, ta ce ta kawo wa shugaba Buhari ziyara ne domin ta gode masa kan irin goyon bayan da yake badawa kan batutuwan da suka shafi masu nakasa.

Harkar tsaro na kara shiga cikin ruɗani a kowace rana a Najeriya musamman yankin Arewacin Najeriya sakamakon ayyukan ta’addanci da ke addabar yankin, inda Boko Haram ke addabar yankin Arewa maso gabashin kasar yayin da Fulani ‘yan bindiga ke addabar yankin Arewa maso yammacin kasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply