Ta’addanci: ISWAP Sun Hallaka Sojoji Goma A Borno

Mayakan ISWAP dauke da bindigogi da kananan bama-bamai a ranar Talata, sun budewa wata tawagar sojoji wuta a hanyarsu na rabon kayayyaki, a garin Marte da ke yankin tafkin Chadi.

“Yan ta’addan sun kashe sojoji 10, ciki harda manyan jami’ai biyu, a harin bazatan,” kamar yadda daya daga majiyoyin ta sanar da AFP.

Hakazalika majiyar ta bayyana cewa sojoji takwas sun jikkata a harin.

Tawagar na a hanyarsu na zuwa kai wa dakarun sojin da ke yankin abinci da sauran kayayyaki lokacin da aka kai masu hari, in ji majiyar wacce ta nemi a boye sunanta.

An kuma tattaro cewa ‘yan ta’addan sun sace kayayyakin abincin sannan suka sanya wa manyan motoci biyu wuta kafin suka tsere cikin jeji.

Sun bayyana cewa harin na iya zama ramuwar gayya ga tayar da sansanin ‘yan ta’addan da aka yi a yankin Marte, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mambobinsu da dama, ciki harda kwamandoji uku.

Mayakan ISWAP dai sun balle ne daga Boko Haram a 2016.

Labarai Makamanta

Leave a Reply