Mashahurin Malamin addinin Musulunci nan mazaunin garin Kaduna Dr Ahmad Gumi, ya bayyana cewar rashin adalci ne idan aka kwatanta ayyukan makiyaya da na ‘yan asalin yankin Biafra (IPOB).
Malamin, wanda aka san shi da samun damar zama da yan fashi da makami, ya ce laifukan makiyaya ko kusa basu kai na IPOB ba ma za’a haɗa ba.
Sheikh Gumi ya ce makiyaya suna satar yara ne kawai don kudi yayinda yan IPOB ke kashe jami’an tsaro da sauran jama’a waɗanda ba su ji basu gani ba.
Da yake magana a shirin gidan talabijin na Arise TV a ranar Laraba, Gumi ya yi kira da adalci a wajen kwatanta kungiyoyin biyu. Ya ce daya “yana kashe mana gwanayenmu yayin da dayan yake satar yara don neman kudi ba kashe su ba”.
“IPOB na kai hari ga‘ yan sanda, sojoji, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da sauran cibiyoyin gwamnati; suna kashe mutanenmu da ke aiki,” in ji shi. ”Sannan makiyaya suna satar yara ne ba don su kashe su ba sai don neman kudi; don haka ta yaya zaku kwatanta wani wanda yake kashe jarumanmu kai tsaye da wanda ke satar yara don neman kuɗi ba kashe su ba.