Rahotanni daga Masarautar Muri Jalingo Jihar Taraba na bayyana cewar mai Martaba Sarkin Muri, Alhaji Abbas Njidda Tafida ya umurci mutanen masarautarsa su yi fito-na-fito da masu garkuwa da mutane da yan bindiga a maimakon su rika tserewa idan sun kawo musu hari, domin kawo karshen matsalar.
Sarkin ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis 13 ga watan Mayu a lokacin da mutane suka kai masa gaisuwar sallah yana mai cewa bata garin da ke adabar mutane kalilan ne idan aka kwatanta su da mutanen gari.
“Idan sun kashe wani a unguwanku, ku mayar da martani ku kashe su ba tserewa za ku yi ba ku kyallesu su kashe ku ko kuma su sace mutanenku,” in ji shi.
“Ya kamata jama’ar gari su daina yarda da harin da masu garkuwa ke kai musu ta hanyar yin fito-na-fito da su duk lokacin da suka kawo hari.”
Sarkin ya kuma bada shawarar cewa a gina ganuwa a iyakokin kauyuka da birane saboda kariya kamar yadda ake yi a zamanin iyaye da kakanni. Ya umurci mutane su rika zama cikin shiri su kuma sa ido a garuwansu.