Mayakan ta’addanci na Boko Haram sun kai hari wani babban barikin sojoji da ke garin Maiduguri, a jihar Borno.
Majiya daga rundunar sojin ta sanar da jaridar The Cable cewa mayakan sun isa garin wurin karfe 11:20 na dare a ranar Litinin inda suka fara harbe-harbe zuwa cikin barikin.
Ba tare da bata lokaci ba dakarun sojin suka fara mayar da martani amma sai dai tuni mayakan ta’addancin sun zagaye barikin, wata majiya ta tabbatar.
Tun farko dai mayakan Boko Haram sun fara kai hari wasu sassa na garin kafin daga bisani su isa barikin. A yayin rubuta wannan rahoton, ana fafata yaki tsakanin ‘yan ta’addan da sojojin.