‘Yan Majalisar Tarayya a karkashin jam’iyyar PDP, sun gargadi Shugaba Muhammadu Buhari cewa idan ba a daina kulla musu sharri ba, kuma bai samar da cikakken tsaro a kasar nan ba, to za su fara shirye-shiryen tsige shi.
Shugaban Kungiyar Mambobin PDP a Majalisar Tarayya, Kingsley Chinda, shi ne ya bayyana haka a ranar Litinin inda ya ce wata daya kacal suka bai wa Buhari, ko ya samar da tsaro ki kuma su tsige shi, domin dawo da martabar kasar nan daga yadda mulkin Buhari ke zubar wa kasar martaba a idon duniya, sakamakon gagarimar satar kudade da ake rincimin fallasawa a Hukumar NDDC da Hukumar EFCC.
Kafin a tsige Shugaban Kasa dai sai an samu amincewar kashi 2/3 na Wakilan Tarayya da Sanatoci.
Gaba dayan su dai su 469 ne, PDP na da 174 ita kuma APC na da 274.
Sun yi korafin yadda masu rike da mukaman da Buhari ya nada ke raina Majalisar Tarayya. Har suka buga misalai da Karamin Ministan Kwadago Festus Keyamo da Shugaban Hukumar NDDC.
Sun kuma nuna damuwa dangane da yawan kashe-kashe a kasar nan.
“Harkar tsaro ta kai ganiyar lalacewa, ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga sun kwace yankunan cikin kasar nan da dama. Sun durkusar da Katsina, jihar haihuwar Shugaban Kasa kuma Kwamandan Askarawan Najeriya.”
Sun kuma yi kira ga Shugabannin Majalisar Dattawa da Tarayya su daina zama ‘yan amshin-Shatan Shugaba Buhari.