Taɓarɓarewar Tsaro: ‘Yan Arewa Muna Ruwa – Ɗorayi

Matsalar tashin hankali da ta’addanci a Arewa, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba ta nunka ta mutanen Kudu masu fafutukar ‘EndSars’ sau dubu.

Amma da yake da su da jagororinsu tafiyar su daya, har an gama da bukatarsu.

“To muma idan da gaske muke matsalar ta dame mu, kamar yadda na ga wasu na taya su. Sai mu fito mu hadu akan tamu matsalar ta #EndNorthBanditry”.

A wani labarin na daban kuma a tsakiyar daren jiya Litinin mahara suka dirar wa kauyan Sabuwar Unguwa dake garin Dandume a jihar Katsina, inda maharan suka dauki mutane uku.

Saidai al’ummar garin sun yi ta maza sun jajirce sun kwato su har ma sun samu nasarar kashe daya daga cikin maharan.

Labarai Makamanta