Da alamun abubuwa sun fara tabarbarewa matsalar rashin tsaro a kasar nan yayinda Sojojin Najeriya dari uku da hamsin da shida (356) suka ajiye aikin Soja bisa dalili na gajiya da aikin.
Rahotanni Na nuna cewa da yawa cikin Sojojin da sukayi murabus daga aikin Soja sun kasance wadanda ke yakin Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya.
Akwai wasu kuma dake aiki a wasu yankunan daban,
A yanzu dai hukumar Sojojin Najeriya na fuskantar barazana a dukkan yankunan Arewacin Najeriya.
Yayinda ake fama da yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabas, ana fama da yan bindiga da garkuwa da mutane a Arewa maso yamma, sannan rikicin makiyaya da manoma a tsakiya.
Amma sabanin Sojoji 356 da sukayi murabus sakamakon gajiya da aiki, wasu 24 daban sun yi ritaya saboda son karbar sarauta a kauyukansu, jimillan Soji 380 kenan, majiyar PT ta bayyana.
Majiyar tace: “Dalilin da yawancinsu suka bada shine gajiya da aiki, kuma haka na nuna cewa ran mutane ya fara fita ne saboda rashin ingantaccen shugabanci.”
“Hakan na nuni ga cewa abubuwa sun tabarbare”