Taɓarɓarewar Tsaro: Na Manta Rabona Da Ƙauyen Mu Ndume

Sanatan dake wakiltar Barno Ta Kudu Ali Ndume ya bayyana cewa akalla dattawan Gwoza 75 ne Boko Haram suka yi wa yankan rago cikin dare daya, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ndume ya bayyana haka a taron kwamitin raya yankin Arewa Maso Gabas, da aka yi a Maiduguri ranar Laraba.

Sanata Ndume, ya kara da cewa ‘yan ba a bada labarin abubuwan da suke faruwa a jihar Barno kamar yadda suke faruwa amma abin ya wuce yadda ake fadi a kafafen yada labarai.

A matsayina na Sanata ba zan iya zuwa garin haihuwa na Gwoza ba, saboda babu tsaro. Amma kuma dole mu cigaba da yabawa jami’an tsaron mu domin suna kokarin su saida dole a fadi gaskiya. Wannan matsala na Boko Haram ya fi karfin jami’an dake kasa.

Akwai ranar da Boko Haram suka tara wasu dattawan Gwoza har 75, suka tafi da su kwata, mahauta, suka rika yanka su kamar raguna. In takaice muku zance dai biyu ne cikin su suka tsira domin a wajen ajiye gawar wadanda suka yanka sun dauka sun yanka su suma.

Haka kuma akwai ranar da suka tara wasu matasa masu yawa, suka harbe su duka. Sannan kuma yunwa ma kawai da ya gama da mutane badun kungiyoyin agaji da suke aiki a jihar ba.

Ko ayanzu da nake magana da ku, ina tabbatar muku cewa akwai wadanda ke mutuwa. Bafa yara ba nake nufi, manya saboda tsanannin yunwa.

Nine na kirkiro kidirin kafa Hukumar Raya yankin Arewa Maso Gabas, kuma muna yabawa hukumar bisa ayyukan da ta ke yi.Saidai kuma kudaden da ke asusun hukumar ba zai iya wadata ayyuka a jihar Barno ba kawai, ballantana sauran jihohin dake yankin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply