Tsohon ‘dan majalisar dattawa mai wakiltan mazabar kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya ce ‘yan majalisar wakilai ta tarayya na tsoron shugaba Muhammadu Buhari duba da kin amsa gayyatarsu da shugaban ya yi.
Yayin da yake zantawa da BBC Hausa, ya jaddada bukatuwar bayyanar shugaban a majalisar don amsa tambayoyi kan harkokin tsaron kasar.
Ya shaida cewa ba su da wata hujja da za su janye kudirin kiran shugaban kasar bayan sun sanar da duniya.
“Kullum mutane na rasa rayukansu da dukiyoyinsu, ana sace su amma fadar shugaban kasa ba ta damuba,6 saboda haka ni banga dalilin da za su janye gayyatar shugaban kasar gaban majalisar ba bayan sun kirashi” a cewarsa.
Ya kuma kara da cewa, Majalisar tarayya ce wurin da ya kamata su isar da koken al’umma su kuma kula da kiyaye muradan yan kasa.
Kun yarda da wannan bayani na Shehu Sani ?
Zamu so jin ra’ayoyinku a shafin mu na muryar yanci/Facebook/Twitter da Instagram.