Taɓarɓarewar Tsaro: An Buƙaci Buhari Da El Rufa’i Su Yi Murabus

Wata kungiya mai fafutukar kare ‘yancin dimokradiyya da hakkin bil adama a Najeriya mai suna Concerned Nigerians ta yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da su yi murabus.

A cikin wata sanarwar da kungiyar ta aikewa ‘yan jarida a yau Litinin kungiyar ta jaddada muhimmancin kawo karshen kashe-kashen da ake ta fama da su a kudancin jihar Kaduna.

Concerned Nigerians ta yi Allah wadai da abin da ta kira sakaci daga gwamnati. A cewarta “kashe-kashen da ake ci gaba da yi a Kaduna ba tare da martanin kirki daga gwamnati abin mamaki ne da Allah wadai.”

Sanarwar ta kara da cewa “a ganinmu dukannin rayukan ‘yan Najeriya na da muhimmanci, ba ma goyon bayan yadda ake ta kashe mutane a Kaduna cikin makonnin da suka gabata.”

Kan wannan zancen, Muryar Amurka ta tuntubi mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmed kuma ya sheda mana cewa “gwamnati na iya kokarinta domin kawo karshen wadannan matsalolin.”

“Wadannan maharan ba mu san ko su waye ba, suna iya sanya tufafi domin sajewa da mutanen gari shi ya sa dole sai mun bi a hankali domin yin abin da ya fi dacewa.”

Ahmed ya kara da cewa, “kan wadannan hare-haren babban hafsan hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai ya je Kaduna domin ganin wadanda lamarin ya shafa.”

Wannan sanarwar ta Concerned Nigerians na zuwa ne kwana daya bayan da jaridu suka rawaito cewa an sake kai wani harin a kudancin jihar ta Kaduna wacce ke fama da matsalar hare-hare.

Labarai Makamanta

Leave a Reply