Taɓarɓarewar Tsaro: Abubuwa Sun Yi Sauƙi A Arewa – Tambuwal

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yace ayyukan ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane sunyi sauki sosai a yankin Arewa masu Yammacin Najeriya.

Gwamnan yayi wan nan furucin ne a yayin da tawagar shugaban Jam’iyyar PDP Uche Secondus ta kawo ziyara a Jihar Bauchi a ranar Jumma’a da yammaci.

Aminu Tambawula ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sama ma jami’an tsaron Najeriya kayan yaki irin na zamani domin kawo karshen tashin tashina a yankin da ma sauran sassan Najeriya.

Hakan nan Gwamnan ya ƙara da cewa “magana ta gaskiya abubuwa sun lafa sunyi sauki sosai musamman a jihar Sokoto, Zamfara, da Kebbi amma a jihar Katsina da Kaduna akwai inda ya dan yi tsamari, mun sami zaman lafiya a gabashin Sokoto inda yafi kamari a da”

Kana ya kara kira ga gwamnatin tarayya da cewa “ta kara daukan mataki na diban jami’an tsaro domin muna da matasa a ko’ina a cikin wan nan kasa basu da ayyukanyi, da yawan su sun chan chanta, ko soja ko dan sanda, ko civil defence ko SSS, immigration, customs ga sunan dai, muna rokon shugaban kasa da yaji kiraye kirayen da ake yi masa”.

Ana shi bayanin kan makasudin ziyarar su zuwa jihar Bauchi Shugaban Jamiyyar PDP Uche Secodus yace sunzo su gana da gwamnan kan irin shugabancinsa a jihar, da kuma tattauna wa irin ta cikin gida,

Da aka tambaye shi kan batun takarar 2023 sai yace, “Jam’iyyarmu tana da tsari babu fifiko, kowa ya chanchanta ya fito takara, tsoho gwamna da mai ci duka daya ne, in kaci ka zama dan takarar jamiyyar mu ta PDP”

Hakan nan shugaban tsare tsare na yankin arewa maso gabas Sanata Nazif yace suna yabawa gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed kan ayyukan da ya bude na cigaban alummar jihar baki daya, yace ya zama dole su jinjina mishi.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply