Taƙaitaccen Tarihin Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris, an haife shi ne a watan Maris na shekarar 1936. Wanda ya haife shi shine Mai Unguwa Auta. Sunan na Auta aka fi sani, amma sunansa na Littafi shi ne Idrisu. Shi ɗa ne, ɗan autan Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo.

Shi kuma Sarki Muhammadu Sambo ɗa ne, kuma na biyu a cikin ‘ya’yan Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim.

Shi kuma Sarkin Zazzau Malam AbdulKarim shi ne na farko a Daular Fulani ƙarƙashin jaddada addinin musulunci da Shehu Usumanu Ɗanfodiyo ya yi a ƙasar Zazzau, kuma shi ne ya assasa gidan Katsinawa a Sarautar Zazzau.

Shi Mai Martaba Sarki lokacin mahaifinsu yana Mai Unguwa a Unguwar Iya, a nan aka haife shi. Unguwar Iya wata unguwa ce da ke tsakanin Unguwar Durumi da Kuyanbana. A nan ya girma, ya shekara aƙalla bakwai, inda har ya shiga makarantar allo, ya fara karatun addini.

A nan dai Unguwar Iya ya yi makarantar farko da Bature ya gina a cikin birnin Zariya, wadda ake kira ‘Town School one’, ita ce kuma makaranatar ‘Kofar Kuyanbana Local Government Education Primary School’. Yanzu ana ce mata ‘Waziri Lawal Local Government Education Primary School’, a nan ya fara karatu.

Bayan ya gama sai ya tafi Alhudahuda College, lokacin ana kiran makarantar da sunan ‘Middle School’. Daga nan aka yi masa sauyi, ya koma makarantar koyar da malunta a Katsina lokacin ana kiran ta ‘Katsina Teachers’ College’.To, a nan ya koyi aikin koyarwa, wanda ita ce babbar sana’arsa ta farko da ya iya.

Daga baya mai martaba ya sauya daga malamin makaranta ya shiga aikin mulki, wanda har ya je kasar Ostireliya (Australia). Yana cikin ɗaliban farko da ofishin jakadancin Ostireliya suka ɗauki ɗawainiyarsu suka je suka yi karatu na koyon ilimin mulki a ƙasar ta Osireliya

Daga shekarar 1956, ya koyar a wurare daban-daban a cikin garin Zariya da ƙauyuka. Ya koyar a Zangon Aya, ya koyar a Paki, har ya yi hedimasta a Pakin. Ya kuma yi hedimasta a Hancin Kare a makarantar ‘Town School No.3”.

A shekarar 1962 ya koma aikin mulki, lokacin da ya koma ƙarƙashin hukumar ‘NA’ (Native Authority) ta Zariya a zamanin Sarkin Zazzau Aminu, inda ya gwama aiki biyu, wato yana aiki a hukumar ‘NA’, kuma yana aiki a matsayin jami’in sadarwa na hukumar kula da kananan hukumomi da masarautu na jihar Arewa.

Daga baya Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya ba shi mukamin Babban sarakatare na musamman na sarki. Daga nan ne sai aka nada shi sarauta, ya zama wakilin ofis, wato mai daukar nauyin duk abin da ya shafi aikin masarauta a karkashin ‘Native Authority’ a wannan lokacin.

Ya rike wannan mukami na tsawon kamar shekara biyu zuwa uku, sai Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya nada shi hakimin birni da kewaye, mukamin da ya rike na tsawon shekara biyu zuwa uku, yana hakimi. Kuma Dan Madamin Zazzau.

A shekarar 1975 likafarsa ta yi gaba, aka naɗa shi sarautar Sarkin Zazzau.

Ya lashe shekaru 45 yana Sarautar Zazzau, ya rasu a ranar Lahadi 20 ga watan Satumba shekara ta 2020 yana da shekaru 84. Allah Muke Roko Ya Jiƙansa Ya Gafarta Mishi Allahumma Amin!!?

Labarai Makamanta

Leave a Reply