Babban Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele ya gargadi Gwamnatin Tarayya kan ba Sheikh Ahmed Gumi damar jagorantar sulhu da ‘yan bindiga.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa ya fitar, Osho Oluwatosin a ranar Alhamis 14 ga watan Maris. Ya ce bai dace a ce farar hula ya na jagorantar sulhu da ‘yan ta’adda ba har sai dai idan ya na tare da su ko su na aiki tare.
Yakara da cewa ba Gumi wannan dama zai kara yawan sace-sacen ne da biyan kudin fansa Ayodele ya ba Shugaba Tinubu shawara da ya binciki Sheikh Gumi saboda sanin mu’amalarsa da ‘yan bindigan har ya sansu.
Faston ya ce ‘yan Najeriya ne suke da damar tallafawa jami’an tsaro domin tabbatar da kawo karshen matsalar tsaro a kasar. Faston ya yi wannan gargadi ne yayin da Shehin malamin ya ce a shirye ya ke domin jagorantar sulhu da ‘yan bindiga.