Sukar Tinubu Ga Ɗan Takarar Mu Abin Dariya Ne – PDP

Jam’iyyar PDP tayi dariya da taga wani faifan bidiyan da jagoran APC ,Asiwaju Bola Tinubu ,inda yake kokarin hana dumukuradiyya tayi aikin ta inda yake nunawa mutane kamar bayinsa ne ,ko Allansu , inda yake kokarin zabawa mutanan Edo mutumin da zai jagorancesu .

Muna mamakin yadda Asiwaju yake nunawa yan Najeriya isa da iko kamar shine ya kawo dumukuradiyya kasar nan,wanda kuma ba haka bane,inda mafi lokaci ma yake tozarta dumukuradiyya ta hanyar kin barin mutane su zabi abun da suke kauna, ya musu karya,yake yaudararsu ta hanyar nuna musu isa da gadara a faifan bidiyan.

Abun mamakine mutumin da yake ganin kamar yafi kowa dumukuradiyya ya zauna a gidan sa yana cin mutuncin mutanan Edo da suke kaunar gwamna Obaseki ya kara wasu shekara hudu masu zuwa ,saboda abubuwan alkhairin da yayi musu .

Asiwaju bai kamata ya cigaba da kiran kansa da jagora ba tunda yana nemawa mutumin da mutanan Edo basu gamsu da nagartar sa ba goyon baya,bayan tsohon shugaban jam’iyyar su, Adams Oshiomhole,yace mar barawo,malamun cocin karya, ya watsa wani dafi,bashi da dabi’a mai kyau, bai kamata ya zama gwamna ba a jahar Edo ba.

Mun San Asiwaju basai ya amince yayi irin wadannan abubuwan nan ba a matsayin sa na Wanda yake so kasa ta amince dashi ba yana yiwa makaryaci yakin neman zabe,ko dan yanason ya shiga ofis?

Ya kamata Asiwaju ya sani Edo sun waye bazasu yadda da rudun da yakewa sauran mutane ba.

Edo jahace ta masu ilimi da tunani suna da tsayyan sarki , addini, da jagorori, da wayewa, manyan yan siyasa da manyan yan kasuwa, Wanda bazasu yadda gwamna Obaseki ya fadi ba.

Idan akwai , abun da Asiwaju yake son fadawa mutanan Edo ,bai wuce siyasar ubangida ba wacce mutanan Edo suke da yakinin kawo karshen ta a jahar ba, Wanda irin wannan siyasar Asiwaju yake a Najeriya a yanzu.

Dadin dawa, muna da bukatar mu sani , muna da tambaya,wani cigaba ya kawo wa dumukuradiyyar tun hawan shugaban kasa Janaral Buhari , ga yan Najeriya tun 2015?

Tabbas, mutanan Najeriya suna ganin wannan ikirarin na Asiwaju na kare dumukuradiyya a matsayin shirme.cikakkun yan kishin dumukuradiyya ne suka kafa jam’iyyar mu kuma suka mulki yan Najeriya,ba irinku ku yan bukata,Wanda kuke kokarin durkusar da kasar nan.

Jam’iyyar mu ta sha kira ga Asiwaju ya fita daga sabgogin dan takarar mu amma yaki.

Mutanan Edo sun gama yanke shawarar sake zabar dan takarar mu gwamna Obaseki don haka duk abun da jagororin APC zasuyi irinsu Asiwaju, bazasu iya hana afkuwar hakan ba.

Sa hannu

Kola Ologbondiyan
Sakataren watsa labarai

Labarai Makamanta

Leave a Reply