Sukar Musulunci: An Buƙaci Kukah Ya Gaggauta Barin Sokoto

Kungiyar Musulim Solidarity Forum dake jihar Sokoto ta bayyanawa Bishop Kuka cewa ko dai ya daina sukar Musulmai da fadar maganganu mara dadai sannan kuma ya bada hakuri ko kuma ya bar Sokoto.

Shugaban kungiyar, Farfesa Isa Maishanu ya bayyana a sanarwar da suka fitar cewa Bishop Kuka na son kawowa zaman lafiya dake tsakanin Musulmai da kiristocin Sokoto tangarda.

Kungiyar ta kuma gayawa shuwagabannin musulmai cewa su daina nunawa Kuka Kara saboda yana amfani da wannan yana yiwa Musulunci katsalandan.

Kungiyar tace a watan Fabrairu na shekarar 2020 Kuka ya fara zanga-zanga kan kisan wani Kirista da aka wanda ake zargin Boko Haram yi amma ya kasa yin irin hakan kan kisan musulmai da ake zargin Kirostoci da yi a Taraba.

Punch ta ruwaito cewa kungiyar ta tambayi Kuka shin me yake tunanin zai faru idan da an rika mayar masa da martani kan abubuwan da ya rika magana akansu a baya?

Saidai a martanin CAN tace wannan kira barazanane kuma ba zasu amince dashi ba.

Labarai Makamanta