Sukar Gwamnati Ya Fi Ta’addanci Hatsari – Fadar Shugaban Kasa

An bayyana cewar a fili yake sukar Gwamnati ya fi tsanani da kuma hatsari akan ayyukan ta’addanci dangin Boko Haram, ko ayyukan ‘yan Bindiga da ‘yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauransu, domin sukar Gwamnati ka?ai na dagula al’amurra da mayar da hannun agogo baya a ?asa, fiye da yadda ta’addanci ke yi.

Mai magana da yawun fadar Shugaban kasa Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar akan halin da ?asa ke ciki, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Adesina ya ce ba matsalar rashin tsaro kadai Najeriya take fama da ita ba, tana fuskantar “yakin harsuna”. A cewar Adesina, caccaka da kushe da wannan gwamnatin take fuskanta ya yi yawa. Wasu mutane sun sadaukar da rayuwarsu wurin runtse ido daga ganin wani amfani da kokarin wannan gwamnatin.

“Yanzu haka kasarmu tana fama da matsaloli da dama. Najeriya tana fuskantar ta’addanci, rashin tsaro, garkuwa da mutane, fashi da makamai, kashe-kashe da kuma caccaka da kushe,” kamar yadda ya wallafa. “Caccaka da kushe Sabuwar matsala ce dama ta dade kuma tafi duk wasu matsaloli wuyar magani.

Kakakin Shugaban kasar ya kara da cewar yawan sukar Gwamnati ya zarce ta’addanci, rashin tsaro, garkuwa da mutane, fashi da makamai da kashe-kashe da sauransu zama gagarumar matsala.

“Kushe da caccaka sun cutar da Najeriya, shugabancinta, duk wani ma’aikacin gwamnati . Idan ka kuskura ka hau wani mukami, karami ko babba, za ka fuskanci matsaloli kuma zaka zama makiyinsu. “Duk kokarinka babu wanda zai gani.

Ta yuwu kayi kokari kwarai a soja, ka zama janar, ka shugabanci PTF kuma kayi bajimta, yanzu kuma kayi shugabancin kasa a matsayinka na farar hula har sau biyu, ga kushe da caccaka daga harsuna iri-iri kuma duk wasu jaridu suna wallafa mara kyau dangane da kai, tabbas wannan abin takaici ne.

“Kullum kushe da caccaka a Najeriya yana kara yawaita, kuma tun daga Muhammadu Buhari har zuwa kananun kujeru na gwamnati, babu wanda ba a suka.

“Sannan duk wasu masu kiran kansu masu rajin kare hakkin bil’Adama, ‘yan jaridu suna wallafa abubuwan da suka ga dama, gidan talabijin ba a barsu a baya ba, kafafen sada zumuntar zamani ma sun rike wuta sannan duk wani wanda yake rike da babbar waya da ‘yan siyasa suna yadda suka ga dama.

“Sannan hatta malaman addinai suna wa’azi akan duk abinda suka ga dama, suna burin sanya tsana tsakanin al’umma.”

Related posts

Leave a Comment