Hukumar tsaro ta farin kaya ta gayyaci sanannen ɗan kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Dr Mahadi Shehu, domin amsa tambayoyi biyo bayan wasu kalamai da ɗan kasuwar ke yawan furtawa musanman akan batun tsaro na jihar Katsina.
Da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar Litinin ne Dr Mahadi ya bayyana ofishin hukumar da ke garin Kaduna, tare da rakiyar tarin wasu matasa wadanda suke rike da manyan kwalaye waɗanda aka yi wa rubuce rubucen neman adalci, da rera wakokin yabo da jinjina gareshi.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala ganawa da jami’an hukumar, Dr Mahadi Shehu ya bayyana cewar ya amsa gayyatar Hukumar matsayin shi na ɗan ƙasa mai biyayya, duk da cewar a farko an bukace shi ne da ya bayyana a ranar asabar, amma ya tabbatar musu ba zai zo a ranar da ba ta aiki ba, sai aka canza ranar zuwa Litinin.
Ɗan Kasuwar wanda ya shafe kimanin awa guda da rabi yana amsa tambayoyi a gaban hukumar, ya bayyana cewar DSS ba su yi mishi magana akan batun Jihar Katsina ba, amma ya bijiro da batun gare su duba da yadda ake cigaba da wa ka ci, ka tashi da dukiyar jihar bisa ga karya da yaudara ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar Mustafa Inuwa.
Dr Mahadi Shehu ya yi alkawarin cigaba da tona asiri da fallasa dukkanin wani mutumin da ke cutar da jama’a yana kwasar dukiyar su bisa ga zalunci a ko ina a fadin ƙasar nan musamman ma a Jihar Katsina, Jihar shi ta asali.