Sukar Buhari: Ganduje Ya Kori Hadimin Shi

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya dakatar da mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai game da wasu ‘maganganu masu kaushi da ya yi kan Shugaba Muhammadu Buhari a dandalin sada zumunta.’

Kwamishinan watsa labarai na Kano, Muhammad Garba da ya bada sanarwar yau Lahadi da rana ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take.

Ya ce duk da cewa hadimin gwamnan yana da ikon yin tsokaci kan batutuwa don ra’ayinsa, a matsayinsa na mutum mai rike da mukami, yana da wahalar a banbance ra’ayinsa da matsayin gwamnan a kan batutuwa da suka shafi al’umma.

Gwamnan ya gargadi masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati su kiyayye yin maganganu da ka iya tada zaune tsaye da janyo cece-kuce.

Tunda farko Yakasai ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Ban taba ganin gwamnati mara tausayi ba kamar irin ta Buhari. Lokuta da yawa mutane suna shiga mawuyacin hali kuma suna bukatar ya basu kwarin gwiwa cewa yana daukan matakai a kai amma baya yin hakan.

Labarai Makamanta