Shahararren mawakin nan kuma mai shirya wasa, Don Jazzy da fitacciyyar mawakiya Tiwa Savage sun amsa gayyatar da jami’an tsaron DSS su ka yi masu.
Mawakiya Tiwa Savage ta fada hannun DSS ne a sakamakon korafin ‘WeAreTired’ da ta rika yi a watan Agusta game da yawan fyade da ake yi a Najeriya.
A jeringiyar sakonnin da taurariyar ta rika aikawa a shafinta na Twitter, ta jawo hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yawan aukuwar fyade.
Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2020 cewa DSS sun ja-kunnen Don Jazzy da Tiwa Savage a kan sukar gwamnati.
Savage da Don Jazzy sun ziyarci ofishin DSS da ke garin Legas, inda aka gargade su game da irin maganganun da ya kamata su rika yi a dandalin sada zumunta.
Kuma tun daga lokacin da Don Jazzy da Tiwa Savage su ka fada hannun DSS, ba su cigaba da babatu a kafofin sadarwa na zamani kamar yadda su ka saba ba.
Rahoton ya ce an yi wannan ganawa da mawakan ne a ofishin DSS da ke Shangisha a watan Agusta Kuma tun daga lokacin ba a kara jin mawakan sun tada maganar ba.
Kuna ganin wannnan mataki da hukumar DSS ta dauka ya dace kuwa?
Zamu wallafa amsoshin Ku masu muhimmanci a shafin mu na MURYAR YANCI zuwa anjima kadan.