Sukar Buhari: DSS Sun Saki Ghali Na Abba

Hukumar tsaron farin kaya, ta DSS, ta saki tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Ghali Umar Na’abba bayan kwashe sa’o’i biyar a hedkwatarta yau Litinin.

Hukumar ta gayyaci Na’abba ne bayan ya soki Buhari a hirar da ya yi a tashar Channel TV inda ya bayyana yadda kungiyar sa za ta samar da sabuwar Nijeriya.

Kakakin kungiyar National Consultative Front NSF, Dr Tanko Yunusa, ya tabbatar da hakan ga Sahara Reporters.

A ranar Asabar ne Hukumar ta DSS, ta gayyace shi. Saidai sai yau ya amsa gayyatar hukumar inda ya isa ofishin DSS da misalin karfe 12:00 na rana bayan shafe sa’a biyar hukumar ta sake shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply