Sukar Buhari: APC Za Ta Fallasa Asirin Mbaka

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki a ta yi barazanar tona asirin Rabaran Ejike Mbaka saboda kalaman da ya yi na neman shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga kan mulki ko kuma a tsige shi.

Mabaka dai ya yi kiran ne saboda Shugaba Buhari ya gaza shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi sassan Najeriya.

Sai dai a martaninta ga kalaman nasa, APC ta bakin mataimakin sakataren yada labaranta, Yekini Nabena ta gargadi Rabaran Mbaka kan furta kalaman da ka iya janyo tashin hankali a kasar.

“Abin kunya ne a ce malamin coci da ya kamata ya ba da gudummawa wajen shawo kan matsalar amma ya bige da yi wa zababben shugaba barazana saboda wasu bukatunsa kuma yake fakewa da sunan fadin abin da ya damu jama’a.”

“Muna kira ga Mbaka da ya maida hankali kan yi wa jama’a wa’azi sannan ya guji yin magana kamar yan siyasa wanda yake cudanya da su. Idan Mbaka ya samu wani abokin siyasa toh ya rika tura sakonninsa ga yan siyasa.

“Yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari ko dai ya yi murabus ko a tsige shi saboda yanayin da kasar ke ciki rashin tsaron Allah ne. Bai kamata Mbaka ya wuce gona da iri ba saboda akwai abubuwa da dama da za mu fada wa fadar Vatican da Fafaroma kan shi Mbaka,” a cewar Nabena.

Related posts

Leave a Comment