Sukar APC: Ganduje Ya Kori Salihu Yakasai

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya tsige mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai a kan nadin nasa kan ci gaba da kalamai da maganganun marasa dadi wadanda ake ganin sun sabawa gwamnatin Jam’iyyar APC da yake yi wa aiki.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya isar da umarnin gwamnan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce hukuncin zai fara aiki nan take.

Ya ce hadimin ya kasa bambance tsakanin ra’ayin mutum da matsayar hukuma kan al’amuran da suka shafi jama’a don haka ba za a iya barin shi ya ci gaba da aiki a gwamnatin da bai yi imani da ita ba.

Gwamnan ya kuma gargadi masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati da su kiyaye daga yin kalaman da za su iya haifar da rikici.

Labarai Makamanta

Leave a Reply