Sufurin Jirgin Ƙasa: Z A Cigaba Da Jigilar Fasinjoji Kafin Sallah – Minista

Ministan sufuri Chibuike Rotimi Ameachi ya bada umurnin dawo da sufurin jiragin kasa daga Abuja zuwa Kaduna wanda aka dakatar sakamakon bullar cutar covid 19 a karshen watan faburairu.

Ameachi ya umurci hukumar dake kula da jiragen kasa su tabbatar da anbi dokokin kula da matakan kariya daga cutar covid 19 kamin a fara jigilar mutane daga Kaduna zuwa Abuja.

Ma’aikatar Sufuri ta bayyana sabon farashin jigilar matafiya a shafinta na twita kamar haka

Karamin kujera – #3000

Matsakaicin Kujera – #5000

Babban Kujera – # 6000

An samu karin kashi 100 na farashin ne sakamakon kiyaye dokokin kariya daga cutar covid 19, inda a yanzu za a dinga bayar da tazara wurin zama a jirgin inda za a fara daukar mutane kadan a jirgin.

Hukumar ta bayyana cewar matukar bata kara kudin ba, Hukumar za tayi asara musamman idan akayi la’akari da siyan man jirgin, tara wa gwamnati haraji da sauran abubuwan kula da jiragen na yau da kullum.

Labarai Makamanta

Leave a Reply